Shugaba Buhari zai kara karfin wutan Najeriya da megawatt 450

Shugaba Buhari zai kara karfin wutan Najeriya da megawatt 450

- Gwamnatin Buhari ta kara megawatt 450 a wutan lantarkin Najeriya

- Kwanan nan dai tashar Azura da ke cikin Jihar Edo za ta soma aiki

- Ana sa rai bayan an kaddamar da gidan wutan a ga canji sosai a kasar

Mun fahimci cewa za a ga bambanci a harkar wutan lantarki a Najeriya bayan an samar da karin megawatt 450 daga tashar Azura. A da an yi tunani sai karshen shekarar nan ne za a kammala wannan gagarumin aiki da ke cikin Jihar Edo.

Shugaba Buhari zai kara karfin wutan Najeriya da megawatt 450
Tashar azura da ke Kudancin Najeriya na daf da soma aiki

Kwangilar wutan Azura da aka bada da dadewa na daf da zuwa karshe kuma ana sa rai nan da watan gobe za a kaddamar da shi. Gwamnatin Shugaba Buhari tayi kokari wajen ganin an jawo aikin wutan gaba da yadda aka shirya a baya.

KU KARANTA: Buhari ya bayyana wadanda su ka jefa kasa cikin wahala

Yanzu dai abin da Najeriya ta ke rabawa na wuta ya haura megawatt 4000 wanda wani lokacin ya kan zarce hakan. A makon jiya ne gidan wutan na Azura yace su na daf da kammala gama jan wutan da zai ba Najeriya sama da megawatt 450.

Jaridar THISDAY tayi magana da babban Ma’aikacin tashar Mista Edu Okeke a wayar salula wanda ya tabbatar da cewa za a haura da wutan zuwa babban layin wutan lantarkin Najeriya domin a rabawa al’umma domin a rage duhu a kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng