Ku jira shugabancin 2023 domin bazaku iya da Buhari ba – Tsohon gwamna a mulkin soja ga Atiku da sauran masu neman takara
Wani tsohon gwamnan jihar Plateau a mulkin soja a lokacin gwamnatin Ibrahim Babangida, Manjo Janar Aliyu Adu Umar Kama (mai ritaya) ya bukaci wadanda ke kokarin takara akan shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2019 da su tsaya har sai 2023.
Da yake hannunka mai sanda ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido da kuma wani tsohon mataimakin gwamnan babban bankin kasar Kingsley Moghalu da sauransu, Kama yace makauniyar shawara ce ga duk wani mahaluki dake kokarin yin takara da shugaba Buhari a shekara mai zuwa.
Yayi maganan ne a wajen wani taron karramawa da kungiyar dattawan Hoba suka shirya domin karrama babban sakataren gwamnatin tarayya, Boss Gida Mustapha a babban birnin tarayya Abuja, a ranar Asabar.
A cewar tsohon gwamnan, mutanen Hoban a jihar Adamawa suna godiya ga shugaba Buhari day a nada ‘yayansu biyu a matsayin manyan sakataren gwamnati sannan sun sha alwashin ci gaba da marawa gwamnatin Buhari baya.
KU KARANTA KUMA: Maulidin Sheikh Nyass: Ina yi wa yan Tijjanawa bangajiya - Sanata Kwankwaso
Da yake maida martini Boss Mustapha ya sha alwashin aiki nagari a yayinda yake ofis sannan cewa zaiyi aiki ba jib a gani domin tabbatar da cewa mutanensa sunyi alfahari da shi a lokacin da zai kammala wa’adinsa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng