Duk duniya babu inda ake kaunar mahaifinmu kamar Najeriya – Iyalan Sheikh Ibrahim Nyass
Rahotanni dake zuwa mana sun nuna cewa iyalan marigayi Shehun darika, wato Ibrahim Nyass sun nuna tarin godiya ga al’umman Najeriya.
Sun jinjina irin kaunar dake tsakanin mahaifin nasu da al’umman Najeriya.
A cewarsu duk duniya babu inda ake kaunar mahaifinsu Sheikh Ibrahim kamar kasar Najeriya.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da aka gudanar da gagarumin Maulidin Shehun a babban birnin tarayya Abuja.
KU KARANTA KUMA: Kungiyar magoya bayan shugaba Buhari dake kasashen waje sun ziyarci sa a masaukinsa dake birnin Landan (hotuna)
Taron ya samu halartan miliyoyin mutane, inda filin Eagles square ya zamo babu masaka tsinke. Baya ga haka harma ance Shehun ya bayyana a wajen taron a cikin hasken fitilar titi.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng