Dandalin Kannywood: Sa'adiyya Gyale tayi karin haske game da yiwuwar dawowar ta fim

Dandalin Kannywood: Sa'adiyya Gyale tayi karin haske game da yiwuwar dawowar ta fim

Fitacciyar tsohuwar jarumar nan a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood wadda aka fi sani da Sa'adiyya Gyale ta yi karin haske game da yiwuwar dawowar ta shirin harkar fim musamman ma idan tayi na'am da irin rawar da za ta fito.

Mun samu dai cewa jarumar tayi wannan karin hasken ne a yayin wata fira da tayi da wakilin majiyar mu lokacin da aka tambaye ta ko za ta iya fitowa fim a halin yanzu inda ita kuma ta bayar da ansa da cewa ya danganta da irin fim din da kuma rawar da za ta taka.

Dandalin Kannywood: Sa'adiyya Gyale tayi karin haske game da yiwuwar dawowar ta fim
Dandalin Kannywood: Sa'adiyya Gyale tayi karin haske game da yiwuwar dawowar ta fim

KU KARANTA: Yan sanda sun damke yan fim 28 suna bakin aiki a Zariya

Haka ma dai da aka tambayi tsohuwar jarumar ko wace shawara za ta ba sauran mata masu harkar fim sai ta ce ta na yi masu fatan alheri, kuma tana ba su shawara da su rike sana’ar fim da kyau domin samun cin moriyar ta.

Legit.ng dai ta samu cewa a watannin baya ne mijin jarumar ya rasu bayan sun shafe shekaru da dama a tare tare kuma da tara zuri'a ta 'ya'ya.

Haka zalika dai tun kafin nan a shekaru da dama da suka gabata jarumar ta yi aure a lokacin da tauraruwar ta take cikin ganiyar haskawa a duniyar shiya fina-finai.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng