An karbe manyan bindigogi sama da 100 a hannu bata-gari a Neja
- Jami’an tsaro sun yi ram da masu kera mugayen makamai a Jihar Neja
- An yi nasarar karbe bindigogi sama da 100 da kuma harsahi kimanin 80
- Gwamnatin Shugaba Buhari na yaki da masu safarar migayun makamai
Mun samu labari cewa Jami’an tsaron ‘Yan Sandan Najeriya sun gano inda ake kera mugayen makamai a wani Kauye mai suna Mashegu a cikin Jihar Neja inda yanzu har an shiga Kotu.
Kamar yadda labari yake zuwa mana daga Jaridar Punch Jami’an ‘Yan Sandan kasar nan sun kama wasu da ake zargi da laifin kera mugayen makamai a Najeriya. Yanzu haka an maka su Kotu domin su zama darasi ga jama’a.
KU KARANTA: Jama’an Zakzaky sun cika tituna da zanga-zanga a Najeriya
Rundunar ‘Yan Sandan kasar kamar yadda Kakakin su na Yankin Jihar Neja Muhammad Abubakar ya bayyana sun karbe bindigogi sama da kala 100 da harsashi iri-iri. Yanzu dai ana cigaba da yakar miyagu a kasar.
A baya dai Sufetan ‘Yan Sandan kasar Ibrahim K. Idris ya haramta amfani da duk wasu makaman da aka kera ba bisa doka ba. A dalilin haka ne ake samun yawitar hare-hare iri-iri a Yankuna da dama na kasar irin su Benuwe da Taraba.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng