Jerin shugabanni 4 mafi karfin mulki a Duniya

Jerin shugabanni 4 mafi karfin mulki a Duniya

A yau fagen kalace-kalace na jaridar Legit.ng ya kalato muku jerin shugabannin wasu kasashe mafi karfin iko a duniya. Wannan shugabanni bincike ya tabbatar da cewa ba bu wani shugaba a duniya da ya kere mu su ta fuskar karfin mulki.

1. Vladimir Putin

Kamar yadda kididdigar mujallar Forbes ta tabbatar, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, ya ciri tuta ta fuskar karfin mulki da kujerar da ba shi dama. Tarihi ya bayyana cewa an haife shi na a shekarar 1952.

Valdmir Putin

Valdmir Putin

2. Donald J. Trump

Shugaban kasar Amurka, Mista Donald Trump da aka haifa a shekarar 1946 shine a sahu na biyu ta fuskar karfin mulki.

Donald Trump

Donald Trump

3. Angela Merkel

An haifi shugaban kasar Jamus, Angela Merkel a shekarar 1954 da ta kasance a sahu na uku cikin jerin shugabannin masu karfin iko. Ta kasance a wannan kujera tun a shekarar 2005.

Angela Merkel

Angela Merkel

KARANTA KUMA: Jerin Mawaka 10 da suka fi kowa kudi a duniya

4. Xi Jinping

An haifi Xi Jinping a shekarar 1953 wanda a halin yanzu shine shugaban kasar Sin. Binciken mujallar Forbes ya tabbatar da shi a sahu na hudu cikin jerin shugabannin duniya mafi karfin mulki.

Xi Jinping

Xi Jinping

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel