Kowa ma ya sani wallahi miliyan 50 Atiku ya bani – Fati Mohammed ga magoya bayan Buhari
Tsohuwar shahararriyar jarumar kamfanin shirya fina-finan Hausa na Kannywood, Fati Mohammed tayi raddi ga magoya bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Ta bayyana cewa babu makawa miliyan 50 tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bata domin yi masa kamfen.
Inda tace duk masu zage-zage wanene ya ji shigar kudi a asusun sa. Ta kuma ce me zaa yi da Buhari da baya bad a ko sisi.
Ta wallafa a shafinta kamar haka: “Kowa ma ya sani wallahi miliyan Hamsin (N50 Million) Atiku ya bani.
“Duk masu zage zage waye ya ji nalert irin nawa.
KU KARANTA KUMA: To jama’a Allah yayi dare gari ya waye, yanzu zamu fara gwagwarmaya da yayan Baba Buhari – Inji Ummi Zeezee
“Me ake yi da Buhari ko sisi baku samu wajen shi.
“Don Allah ko ku ne kuka ji wannan alert in zaku biye wa wani Buhari?”
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng