Sheikh Ibrahim Nyass ya bada gagarumin gudunmawa wajen ci gaban addnin Musulunci a duniya — Inji Buhari
Shugaban Kasa Muhammad Buhari ya bayyana cewa Sheikh Ibrahim Inyass jagoran mabiya hanyar darika, ya taka gagarumin rawar gani wajen ci gaban addinin Musulunci a nahiyoyin Afrika, Asiya da Turai.
A cewar shugaban kasar Shehun ya bayar da wannan gudunmawa ne ta hanyar rubuce rubucensa.
Buhari ya bayyana hakan ne a yayin bikin Maulidin wanda aka gudanar a babban birnin tarayya Abuja a ranar Asabar 14 ga watan Afrilu.
KU KARANTA KUMA: Jam'iyyar PDP ta baiwa Ummi Zeezee babban mukami
Ministan Ilimi, Adamu Adamu ne ya wakilce shugaban kasar inda ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da bayar da hadin kai ga mabiya Darikar Tijjaniyya don wanzuwar zaman lafiya a kasa sannan ya nemi a ci gaba da yi wa Nijeriya Addu'o'i.
A halin da ake ciki., Tsohuwar shahariyyar jarumar Kannywood, Ummi Ibrahim Zeeze tayi raddi ga magoya bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Tace yanzu zasu fara gwagwarmaya da yayan shugaban kasar domin ganin yadda zata kaya a zaben 2019.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng