Jam'iyyar PDP ta baiwa Ummi Zeezee babban mukami
Rahotanni sun kawo cewa babban jam’iyyar adawan Najeriya, PDP ta baiwa tsohuwar jarumar fina-finan Hausa na Kannywood, Ummi Zeezee babban mukami.
An bata mukamin shugabar riko ta mata ta kungiyar dake yiwa PDP kamfe gida-gida ta kasa baki daya.
Ummi da take bayyana hakan a shafinta na sada zumunta da muhawara tace ta godewa Allah da wannan mukami da ta samu yau, kuma tana fatan Allah ya baiwa jam'iyyar ta PDP mulki a zaben shekarar 2019.
Ummi dai tayi suna wajan caccakar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.
KU KARANTA KUMA: Kalli hotunan yadda dandalin taro na Eagles Square ya cika ya tunbatsa sakamakon Maulidin Sheikh Ibrahim Nyass
Hakazalika shugaban kungiyar yiwa PDP kamfen gida-gida na kasa, Ibrahim Dahiru Danfulani ya tabbatar da wannan mukami na Ummi Zeezee a jiya Juma'a.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng