Gabas ta tsakiya ta dauki dumi, bayan hare-haren Amurka da kawayenta kan Siriya
- Gabas ta tsakiya cike take da mussulmi
- Siyasar yankin tafi ta kowanne yanki saurin tafasa
- An fara kai wa kasar hari bayan zargin Assad da amfani da makamai masu guba
Siyasar gabas ta tsakiya ta dauki dumi bayan da shugaba Trump ya hado kan kawayensa domin kaiwa kasar Siriya hare-hare ta sama. Inda ita kuma kasar Rasha da Iran suka sha alwashin kare gwamnatin ta Assad din, wadda ke cikin yaki tun 2011.
Matakan dai da turawan suka dauka, sun biyo bayan hare-haren da shugaba Assad din ya kai wa unguwannin 'yan tawaye da makamai masu guba, irin wadanda duniya ta haramta amfani dasu tun bayan da Saddam Hussain yayi amfani da irinsu ya kashe 'yan kasarsa masu tayar da kayar baya ga mulkinsa a 1980s.
DUBA WANNAN: Mun dakatar da sulhu da Boko Haram - Buhari
Wasu bangarorin na larabawan dai, suna tare da Amurka, musamman Saudiyya da kawayenta 'yan Sunni, sai kuma bangaren Shi'a, wadanda Iran ke mara wa baya, a Yemen da Lebanoon da ma Iraqi, wadanda suke ganin Assad din namijin zaki ne.
A yanzu dai larabawa da yawa sun dawo daga rakiyar azzaluma shugabanninsu masu iya kashe 'yan kasarsu muddin suka ce sun gaji da mulkin dangi daya a kasar su.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng