Dandalin Kannywood: Jaruma Umma Shehu tayi tsokaci game da firar ta da Aminu Momo
Shahararriyar jarumar nan ta wasannin fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood watau Umma Shehu a karon farko ta fito tayi tsokaci game da firar da tayi da fitaccen dan fim din nan, ma'aikacin tashar tauraron dan adam ta Arewa24, watau Aminu Sharif Momo a watannin baya.
KU KARANTA: Rahama Sadau tayi karin haske game da wanda zata aura
Jarumar dai ta bayyana cewa ita ba ta ji haushi ba ko kadan bisa ga tambayar da yayi mata a wani shirin Kundin Kannywood game da lamarin addini domin a cewar ta suna fira ne ita kan nishadantarwa.
"Duk wanda ya kalli wannan firar ya san wasa ne da dariya a cikin sa" a cewar ta.
Legit.ng ta samu cewa kuma jarumar ta ayyana cewa ita bata da kawa a cikin masu shirya fina-finan don kuwa a cewar ta ba ta son dukkan wani abun da zai zo ya bata mata rai.
Da aka tambaye ta ko wani irin kalubale ne ta ke fuskanta a sana'ar ta ta sai jarumar ta ce ita tun da ta shiga harkar ba ta fuskantar kalubale sai dai alheri tun da ta shiga.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng