Kalli hotunan yadda ake aikin fadada kewayen Masallacin Harami a birnin Makkah
A daidai lokacin da azumi ke gabatowa, a birnin Makkah na kasar Saudiyya kuwa aiki ne ya kankama.
Ana aikin ne domin fadada kewayen Masallacin Harami wanda ke birnin.
Wannan aikin fadada Titin Ibrahim Al-Khalil ne, wanda ke da tazarar mita 150 daga Masallacin.
A lokacin azumi birnin Makkah kan cika ya tunbatsa day an aikin Umurah. Sannan kuma kamar yadda kuka sani azumi bashi da takara sosai da lokacin aikin hajji.
KU KARANTA KUMA: Shugaban ‘yan kato da gora yace an gana masa azaba akan yayiwa Shehu Sani Sharri
Wannan yasa a kullun birnin Makkah cike yake da sababbin kawa da kwalliya, inda har anyi has ashen cewa da mutun zai dunga zuwa birnin a duk wata toh sai ya ga sababbin sauye-sauye.
Ga hotunan a kasa:
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng