Kotu ce za ta raba mu da Gwamna M.A idan bai sake fitowa takara ba - Inji Al'ummar Jihar Bauchi

Kotu ce za ta raba mu da Gwamna M.A idan bai sake fitowa takara ba - Inji Al'ummar Jihar Bauchi

Rahotanni sun kawo cewa wasu tawaga masu goyon bayan gwamnan jihar Bauchi Barista M.A Abubakar sun sha alwashin kai karar gwamnan Kotu idan har yaki sake fitowa takara a zaben 2019.

Tawagar dake son ganin ya sake fito takara wanda mafi yawan su matasa ne, sun bayyana cewa sun dauki kudirin sake zaben gwamnan domin ganin ya ci gaba da gudanar da ayyukan cigaban da ya soma a mulkinsa na farko. Wanda ko masu adawa da gwamnatin ma sun gani a kasa.

"Ayyukan gwamna M.A ya karade ko ina a jihar Bauchi kama daga birane da kauyuka, don haka ba mu da gwanin da ya kamaci ya ci gaba da jan ragamar shugabancin jihar Bauchi kamar Barista M.A Abubakar.

KU KARANTA KUMA: Shugaban ‘yan kato da gora yace an gana masa azaba akan yayiwa Shehu Sani Sharri

"Kama daga bagarorin ilmi, lafiya, raya karkara, samar da ayyukan yi, warware matsalar rashin biyan albashin ma'aikata, babu inda Gwamnan bai kawo ci gaba ba", kamar yadda daga cikin magoya bayan gwamnan suka bayyana.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng