Tsofaffin ‘yan PDP kamar su Atiku, Kwankwaso, Saraki sune suka doraka kujerar shugaban kasa – Lamido ga Buhari

Tsofaffin ‘yan PDP kamar su Atiku, Kwankwaso, Saraki sune suka doraka kujerar shugaban kasa – Lamido ga Buhari

- Sule Lamido dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, yace daba dan tsofaffin ‘yan PDP da suka koma APC ba, da shugaba Buhari baici zaben 2015 ba

- Lamido a ranar juma’a ya bayyana cewa baya tsoron sake tsayawar Buhari takara a zaben 2019

- Lamido yace Buhari ya bayyana kudurinsa na sake tsayawar takara bayan taronsu

Sule Lamido dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, yace daba dan tsofaffin ‘yan PDP da suka koma APC kamarsu Atiku, Kwankwaso, Saraki, ba da shugaba Buhari baici zaben 2015 ba.

Lamido a ranar juma’a ya bayyana cewa baya tsoron sake tsayawar Buhari takara a zaben 2019, yace Buhari ya bayyana kudirinsa na sake tsayawa takara bayan taron mutane da yaji PDP tayi a jiharsa ta Katsina.

Yace duk da cewa Buhari sananne ne amma hakan baisa yaci zabe ba, sai bayan wani jigo na PDP da ya dawo jam’iyyarsu a shekarar 2015 sannan ya samu yayi nasara saboda haka tsoron me zanji nasa.

KU KARANTA KUMA: An gurfanar da wani mutum bisa laifin luwadi da yaro a Kano

Saboda haka Buhari nada damar sake tsayawa takara tinda ‘ya’yanmu suka dorashi wanda kaga ya zama jikanmu kenan, kuma doka ta bashi wannan damar kamar kowane dan Najeriya, amma dai zamu kadashi a zaben na 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel