Shugaban ‘yan kato da gora yace an gana masa azaba akan yayiwa Shehu Sani Sharri
- Ma’aikacin kato da gora (JTF) ya amsa cewa anyi amfani dashi don a yiwa Shehu Sani sharri
- Sanatan ya mayar da murtani ta shafinsa na sadarwa
- Kwamishinan ‘Yan Sanda ya bukaci Shehu Sani yaje helikwatarsu ta Kaduna a ranar 30 ga watan Afirilu akan lamarin
Ma’aikacin kato da gora (JTF) ya amsa cewa anyi amfani dashi don a yiwa Shehu Sani sharri
Sanatan ya mayar da murtani ta shafinsa na sadarwa na Tuwita, inda ya bayyana cewa duk wani kulli da za’ayi a kaina don a bata mani suna bazaiyyi nasara ba.
Garba Isa mamba ne na kato da gora (JTF) a jihar Kaduna, wanda shine yayi jagoranci wurin kisan wani Lawan Maiduna, wanda yace Sojoji ne suka takurashi akan yace da sa hannun Shehu Sani sukayi kisan, ya bayyanawa manema labarai haka ne a ranar Alhamis 12 ga watan Afirilu, a jihar Kano.

Isa ya kara da cewa ya kai sati biyu a hannun Sojoji, amma duk da haka yaki amincewa yayiwa Shehu Sani sharrin da sukeso yayi masa, inda yace sai a kotun jihar Kaduna sannan ya samu aka sakeshi amma dai ya samu raunuka a hannunsa na dama.
KU KARANTA KUMA: Tsofaffin ‘yan PDP kamar su Atiku, Kwankwaso, Saraki sune suka doraka kujerar shugaban kasa – Lamido ga Buhari
Kwamishinan ‘Yan Sanda ya bukaci Shehu Sani yaje helikwatarsu ta Kaduna a ranar 30 ga watan Afirilu, don ya amsa wasu tambayoyi da yakeso ya masa akan lamarin.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng