An gurfanar da wani mutum bisa laifin luwadi da yaro a Kano

An gurfanar da wani mutum bisa laifin luwadi da yaro a Kano

- Kotu ta daure wani mutum mai suna Baffa Sani, a jihar Kano, sakamakon luwadi da yayi da wani yaro dan shekara 10

- Sani dan unguwar Kurawa ne a jihar Kano, yana kuma fuskantar shari’a duk da dai bai amsa laifin nasa da ake zarginsa dashi ba

- Alkalin Muhammad Jibril, ya bayar da umurnin cigaba da tsare wanda ake zargin har zuwa lokaci na gaba da za’a cigaba da shari’ar

Kotu ta daure wani mutum mai suna Baffa Sani, a jihar Kano, sakamakon luwadi da yayi da wani yaro dan shekara 10.

Sani dan unguwar Kurawa ne a jihar Kano, yana kuma fuskantar shari’a duk da dai bai amsa laifin nasa da ake zarginsa da aikatawa ba.

Alkalin Muhammad Jibril, ya bayar da umurnin cigaba da tsare wanda ake zargin har zuwa lokaci nagaba da za’a cigaba da shari’ar shine ranar 30 ga watan Afirilu.

An gurfanar da wani mutum bisa laifin luwadi da yaro a Kano
An gurfanar da wani mutum bisa laifin luwadi da yaro a Kano

Mai gabatar da kara Speto Pogu Lale, ya bayyanawa kotu cewa a ranar 20 ga watan Maris, Awaisu Ibrahim na Tudun Wuzurci a Kano, ya kawo rahoton a Helikwatar Ofishin ‘Yan Sanda na Mandawari, a jihar kano.

KU KARANTA KUMA: Atiku ya sake kira ga yiwa Najeriya gyara

Lale yace wanda ake zargin yaja yaron kanin wanda ya kawo kara da misalin karfe 1:30 na rana bayan ya dawo daga makaranta yayi luwadi dashi a cikin wani kango na unguwar Kurawa a Kano, wanda laifin ya sabawa sashe na 284 na doka.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng