Wata daliba ta kone yayinda ta tafi Coci neman addu'ar nasarar jarabawa
- Wata dalibar ajin karshe a sakandire, Efua Asentewa, ta hadu da ajalinta yayin ta tafi Coci neman addu'an cin jarabawa
- Limamiyar Cocin, Efua Eguama ta malale tufafin yarinyar da mai kuma ta kuna kyandir ta kuma umurci yarinyar ta rike a hannu
- Daga bisani tufafin yarinyar ya kama da wuta inda ya mata mumunan kuna wanda yayi sanadiyar rasuwarta bayan an kai ta asibiti
Wata dalibar ajin karshe na makarantar sakandire ta gamu da ajalinta sakamakon wuta ya kama tufafinta yayinda taje Coci domin ayi mata addu'a na musamman domin samun nasara a jarabawar gama sakandire (WASSCE) da za ta rubuta.
Dalibar mai suna Efua Asantewa yar makarantar Mozana Senior High School da ke yankin Portia Donkor na tsakiya a kasar Ghana ta tafi Cocin ne tare da mahaifiyarta saboda ayi mata addu'a amma daga bisani abubuwa suka rinchabe.
DUBA WANNAN: Hadimin gwamnan Akwa Ibom ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC
Kamar yadda muka samo daga jaridar Punch, Limamiyar African Faith Church na Breman Bedum, Efua Eguama mai shekaru 45 ta malale yarinyar da mai a yayin da take mata addu'o'in kuma daga bisani ta kuna kyandir ta bawa yarinyar ta rike a hannun ta.
Jim kadan bayan mika matan kyandir din sai tufafin yarinyar suka kama da wuta kuma dalilin hakan ta samu munanan kuna a jikinta. An garzaya da ita asibitin Breman Asikuma amma daga baya aka tura su zuwa asibitin koyarwa na Korle Bu inda yarinyar tace ga garinku.
Jami'an Yan sanda sun kama limamiyar cocin inda za'a gurfanar da ita a kotu ranar Talata bisa tuhumar ta da laifin aikata kisan kai. Kwamandan hukumar Yan sanda na yankin Breman Asikuma, ASP Emmanuel Donkor Baah ya tabbatar da afkuwar lamarin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng