Dandalin Kannywood: Babu macen da ta kai 'yar fim dadin aure - Jaruma Ladidi Tubeless
- Babu macen da ta kai 'yar fim dadin aure inji Jaruma Ladidi Fagge
- Ta yi ikirarin ne a yayin wata fira da ta gudanar da wakilin majiyar mu
- abun takaici ne yadda mutane ke yi wa 'yan matan fim din mummunar fahimta
Daya daga cikin fitattun jaruman nan na masana'antar shirya fina-finan Hausa na Kannywood mai fitowa a matsayin uwa wadda Ladidi Abdullahi amma wadda aka fi sani da Ladidi Tube less ta yi ikirarin cewa duk duniya babbu mace mai dadin aure kamar 'yar fim.
KU KARANTA: Rahama Sadau ta ayyana yadda ta rasa budurcin ta
Hajiya Ladidi kamar dai yadda muka samu ta yi wannan ikirarin ne a yayin wata fira da ta gudanar da wakilin majiyar mu a garin Kaduna dake zaman mahaifar ta.
Legit.ng ta samu cewa jarumar ta bayyana cewa abun takaici ne yadda mutane ke yi wa 'yan matan fim din mummunar fahimta musamman ma yadda su ke gudun auren su alhali kuma sun fi kowa dadin aure.
Haka ma dai jarumar da aka bukaci ta bayar da shawara zuwa ga sauran matan da ke harkar fim din sai ta ce "Shawara ta gare su shi ne su yi karatu, saboda na ga gaba abubuwa za su canje wanda zai kai lokaci da sai kana da karatu za ka yi shi kansa fim din ma."
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng