‘Yan Shi’a ku cigaba da zanga-zangar ku - Falana
- Babban Lauya Femi Falana (SAN) ya bukaci kungiyar ‘Yan Shi’a ta IMN, don a sakar musu shugabansu Sheik Ibraheem El-Zakzaky
- Falana yace naji dadi da yanda kuka jajirce wurin yin zanga-zangar lumana, saboda yana cikin cikin doka, wadda ta baku damar yin hakan
- Yace yana so daga su har sauran masoya kada mu bari gwamnatin Buhari ta sabawa umurnin kotu
Babban Lauya Femi Falana (SAN) ya bukaci kungiyar ‘Yan Shi’a ta IMN, don a sakar musu shugabansu Sheik Ibraheem El-Zakzaky.
Falana yace naji dadi da yanda kuka jajirce wurin yin zanga-zangar lumana, saboda yana cikin cikin doka, wadda ta baku damar yin hakan. Saboda kotu ta badaumurnin sakin shugaban naku a sashe na 2 na shekarar 1984.
Falana yace ina bukatar daku da sauran masoya da kada mu bari gwamnatin Buhari ta sabawa umurnin kotu. Kamar yadda kuka sani kotun tarayya, inda Alkali G.O Kolawole ya bayarda umurnin sakin sheikh Ibraheem El-Zakzakiy da matar sa kuma yace a basu N50m, sakamakon lalata masu gida da gamnatin Nasir El-Rufa’i da Sojoji Najeriya sukaiyi.
KU KARANTA KUMA: Taron PDP ne ya firgita Buhari ya ce zai yi takara - Sule Lamido
Amma gwamnatin Buhari tasa kafa ta shure wannan umurni da kotu ta bayar, bayan tana ikirarin cewa gwamnati ce mai aiki da doka. Ina bukatar ku cigaba da wannan zanga zanga har sai gwamnati ta bi umurnin kotu ta sakar maku shugaba.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng