Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un: Yan bindiga sun kashe mutane 22 a jihar Zamfara

Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un: Yan bindiga sun kashe mutane 22 a jihar Zamfara

Akalla mutane 22 ne wasu yan bindiga da ake zargin yaran Buharin Daji ne suka bindige a kauyukan Kuku-kuru da Jarkuka, dukkaninsu a cikin karamar hukumar Anka ta jihar Zamfara.

Yan bindigan sun kai wannan hari ne a ranar Laraba 12 ga watan Afrilu, inda suka bude wutar mai kan uwa da wabi ne akan wasu mutane dake hakar ma’adan kasa, kamar yadda suka yi a kauyen Bawon Daji, kimanin sati biyu da suka gabata, kamar yadda gidan Talabijin na Channels ta ruwaito

KU KARANTA: Jarabawar gwaji: Cikin Malaman makarantun sakandari a jihar Kaduna ya duri ruwa

Legit.ng ta ruwaito wani mazaunin kauyen Ali Yusuf yana fadin yan bindigan sun shirya kai hari a kauyen Kuru-kuru, amma sai jama’an kauyen Jarkuka suka dau alwashin basu agaji, a lokacin da yan bindigan suka fahimci hakan ne sai suka tare jama’an Jarkuka, suke bude musu wuta.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kaakakin rundunar yansandan jihar, DSP Muhammad Shehu ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai yace zuwa yanzu rundunar bata tabbatar da adadin wadanda suka mutu ba.

Wannan hari yazo a daidai lokacin da gwamnatin jihar Zamfara ta kafa wata kwamitin raba kayan tallafi ga jama’an da harin Bawon Daji ya shafa, inda yan bindiga suka kashe mutane da dama.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng