Dandalin Kannywood: An roki shugaba Buhari ya gida gidajen Sinima-Sinima a arewa
Daya daga cikin fitattun daraktoci masu ba da umurni a masana'antar Kannywood mai suna Kamal S. Alkali ya roki shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya ginawa 'yan fim din dake arewacin Najeriya gidajen kallo na zamani.
KU KARANTA: Aina'u Ade ta ayyana ranar auren ta
Fitaccen daraktan wanda kuma marubuci ne ya yi wannan rokon ne a yayin da yake fira da wakilin majiyar mu inda ya bayyana cewa rashin wuraren kallo kayatattu kuma masu yawa ne yake sa sana'ar ta su ba ta cigaba sosai.
Legit.ng ta samu cewa kuma Alhaji Kamal S. Alkali wanda ya karbi kyaututtuka da dama, ya roki gwamnatin tarayya da ta taimaka masu wajen yaki da masu satar fasaha wadanda acewar su suke matukar basu ciwon kai.
Wasu daga cikin fina-finan da fitaccen daraktan dai ya jagoranta sun hada da 'Laila Adnan', 'Sahabi' da kuma 'Umar Sanda'.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng