Fada na neman barkewa a tsakanin kasar Amurka da Rasha

Fada na neman barkewa a tsakanin kasar Amurka da Rasha

Shugaban kasar Amurka Dolad Trump ya yi kakkausan raddi zuwa ga mahukuntan kasar Rasha dangane da alwashin da tayi na kakkabo dukan makamin za ta harba akan Syria.

Shi dai shugaban kasar na Amurka ya bayyana cewa kasar Rasha din ta kwan da shirin cewa yanzu ita ce za ta kai ma hari nan ba da dadewa ba.

Fada na neman barkewa a tsakanin kasar Amurka da Rasha
Fada na neman barkewa a tsakanin kasar Amurka da Rasha

Legit.ng ta samu cewa kasar Amurka da kawayenta suka zargi Shugaban kasar Syria din Bashar al- Assad da yin amfani da makami mai guba akan 'yan tawayen kasar sa.

A wani labarin kuma, Hankula suna ci gaba da tashi musamman ma a tsakanin manyan jami'an gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari sakamakon binciken da babbar kotun duniya ta kasa-da-kasa ta soma yi bisa laifuka har 8.

Mun samu wannan labarin ne dai a ta bakin babban ministan shari'a na gwamnatin Abubakar Malami wanda ya bayyana hakan lokacin da ya karbi bakuncin sabon shugaban kotun ta duniya Farfesa Chile Osuji a ofishin sa garin Abuja.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng