Daliban Najeriya yan Arewa da suka ciri tuta a kasar waje sun dawo gida (hoto)

Daliban Najeriya yan Arewa da suka ciri tuta a kasar waje sun dawo gida (hoto)

Dalibai biyar da suka wakilci Najeriya a wani gasa a kasar Singapore sannan suka yi nasara sun dawo Bauchi a wannan makon.

Daliban sun zamo zakara wajen lashe kofin Oldham Cup Debate Championship tare da sauran dalibai daga kasashen China, Hong Kong, India, Korea da kuma Taiwan.

Sun je kasar Singapore tare da malamai biyu da kuma shugaba daga hukumar makarantu na jihar (SUBEB) inda suka zamo na farko a gasar kasar da ofishin matar shugaban kasa Hajiya Aisha Buhari ta shirya.

Da dawowarsu, daliban da malaman sun samu tarba daga shugaban hukumar SUBEB na jihar, Farfesa Yahaya Ibrahim Yero a hedkwatar hukumar dake Bauchi.

Daliban Najeriya yan Arewa da suka ciri tuta a kasar waje sun dawo gida (hoto)
Daliban Najeriya yan Arewa da suka ciri tuta a kasar waje sun dawo gida

Ya kuma yaba masu bisa namijin kokarin da suka yi wajen daga martabar kasar a idanun duniya.

KU KARANTA KUMA: Dandalin Kannywood: Auren Sadiya Kabala ya zo

Ya kuma yaba ma gamnan jihar Mohammed Abdullahi Abubakar bisa goyon bayan da ya bayar tare da daukar nauyin daliban zuwa Singapore.

Daliban sun hada da Abdulbarri Yahaya daga karamar hukumar Bauchi, Hassan Ali Hassan daga Shira, Hamida Aliyu daga Bauchi, Maryam Ya'u daga Jama'are da kuma Rashida Dauda daga karamar hukumar Dass.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel