Dalilin bayyana kudirina na tsayawa takara kafin tafiyata Ingila – Shugaba Buhari
- Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana kudirinsa na sake tsayawa takarar shugaban kasa ba lokacin da ya tsara ba
- Femi Adesina ya bayyana cewa Buhari ya fada hakane lokacin da ya karbi bakuncin Archbishop Justin Welby a garin London
- Shugaba Buhari yace ya bayyana kudirin nasa ne kafin ya tafi saboda mutanen Najeriya suna ta nuna masa damuwarsu na sunaso su san ko zai tsaya takarar ko bazai tsaya ba
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana kudirinsa na sake tsayawa takarar shugaban kasa ba lokacin da ya tsara ba, soda lamarin ya mamaye siyasar Najeriya.
Femi Adesina mai magana da yawun shugaban kasa, ya bayyana cewa Buhari ya fada hakane lokacin da ya karbi bakuncin Archbishop Justin Welby a birnin London.
Shugaba Buhari yace: “na bayyana kudirin nasa ne kafin ya tafi saboda mutanen Najeriya suna ta nuna masa damuwarsu na sunaso su san ko zai tsaya takarar ko bazai tsaya ba, shiyasa naga cewa ya dace na kawo karshen wannan kace nnace in bayyana kudurina.
“Muna da abubuwa da dama wadanda ya kamata mu mayar da hankalinmu a kansu kamar Tsaro, Noma, Tattalin Arziki, yaki da rashawa, da kuma abubuwa da dama. Duk wadannan abubuwan ya kamata mu mayar da hankali a kansu, kada siyasa ta dauke mana hankali.
KU KARANTA KUMA: Rikicin makiyaya da manoma ya girme mu – Buhari ga babban limami
“Yawancin mutanen Najeriya suna jin dadin ayyukan da mukeyi, wannan shine babban dalilin da ya sanya zan sake tsayawa takara”.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng