Rikicin makiyaya da manoma ya girme mu – Buhari ga babban limami
- Shugaba Buhari yace fadan Makiyaya da Manoma a Najeriya ya girmi gwamnatinsa
- Buhari ya bayyana hakane lokacin da yake amsa tambayar da Reverend Justin Welby yake tambayarsa game da fadan Makiyaya da Manoma a yankunan Najeriya
- Mai bawa shugaban kasa shawara ta fannin labarai yace shugaba Buhari yace abunda ke kawo fadan shine siyasa ta rashin tinani
Shugaba Buhari yace fadan Makiyaya da Manoma a Najeriya ya girmi gwamnatinsa. Shugaban Buhari ya bayyana hakane a ranar Laraba, a garin London, lokacin da yake amsa tambayar da Reverend Justin Welby yake masa game da fadan Makiyaya da Manoma a yankunan Najeriya.
Mai bawa shugaban kasa shawara ta fannin labarai yace shugaba Buhari yace abunda ke kawo fadan shine “siyasa ta rashin tinani”, yace fadan ya dade ana yinsa, kuma yace ana ta kokarin magance matsalar sannan za’a hukunta duk wanda aka samu da laifi.
Game da ‘yar makarantar Dapchi da har yanzu take hannun kungiyar Boko Haram, Leah Sharibu, saboda kin karbar musulunci, shugaban kasar yace anata kokarin karbota har yanzu.
Arcbishop Welby yace a koyaushe yana farin ciki da ganin shugaba Buhari.
KU KARANTA KUMA: Bukar yayi kokarin samun amincewar majalissa akan gina Poly ta tarayya a jihar Katsina kafin rasuwarsa - Sanatoci
Sannan kuma ya tabbatar da goyon bayansa akan shugaba Buhari. Kuma yace zamu cigaba dayi maka addu’a a ko yaushe ya kara tabbatarwa shugaba Buhari.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng