'Yan Bindiga sun kashe mutane 10 a jihar Benuwe

'Yan Bindiga sun kashe mutane 10 a jihar Benuwe

Da sanadin shafin jaridar Daily Trust Legit.ng ta samu rahoton cewa, kimanin rayukan mutane 10 ne suka salwanta a wani harin 'yan bindiga da ya sake afkuwa a wasu kauyuka dake kananan hukumomi biyu a jihar Benuwe.

Jaridar ta ruwaito cewa, ajali ya cimma wadannan mutane ne a wasu hare-hare daban-daban da suka afku a kauyen Gbeji na karamar hukumar Ukum da kuma kauyen Tswarev na karamar hukumar Logo a daren ranar Talatar da ta gabata.

Mazauna yankunan sun bayar da shaidar cewa, maharan sun dirfafi kauyukan ne inda suke bude wuta ta harsashen bidiga a kan al'ummar da ya sanya suka yi aron kafar kare don neman tsira.

'Yan Bindiga sun kashe mutane 10 a jihar Benuwe
'Yan Bindiga sun kashe mutane 10 a jihar Benuwe

Rahotanni sun bayyana cewa, mutane bakwai ne suka riga mu gidan gaskiya a karamar hukumar Gbeji yayin da kuma wasu ukun suka ce ga garin ku nan cikin al'ummar karamar hukumar Logo.

KARANTA KUMA: Mutane 8 sun shiga hannu da laifin fyade 'yar shekara 8 kuma suka ƙone ta da ran ta

Legit.ng ta fahimci cewa, bayan wannan rashin tausayi na mahara da suka aikata, sun kuma kone gidaje da dama cikin harin na su da suka dauki kimanin awanni uku su na ta'addanci.

Shugaban karamar hukumar Logo, Richard Nyajo da kwamshinan 'yan sanda na jihar Fatai Owoseni, sun yi tarayya wajen tabbatar da afkuwar wannan hari.

Owoseni dai ya bayyana cewa, a halin yanzu jami'an sa sun tsinto gawawwaki hudu kuma su nan a bakin aiki domin ci gaba da binciken lamarin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng