Gwamnatin Buhari za ta kashe Biliyan 13 a kan yasar tashar ruwa
- Gwamnatin Shugaba Buhari za ta yashe tashar ruwan da ke Yankin Warri
- Ministan sufiri na kasar ya bayyana wannan bayan taron Ministoci na jiya
- Shugabar Hukumar NPA Bala Usman tace yasar zai taimakawa kasar sosai
Labari ya zo mana a jiyan nan cewa Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari tayi na’am da a kashe Naira Biliyan 13 wajen yasar tashan ruwan nan na Escavos da ke Garin Warri a Jihar Delta.
Ministan sufuri na kasar watau Rt. Hon. Rotimi Amaechi ya bayyana wannan a taron Majalisar zartarwa watau FEC na kasar da aka yi na makon nan jiya a fadar Shugaban kasa a Abuja. Mataimakin Shugaban kasa ya jagoranci taron.
KU KARANTA: Ganduje ya bayyana dalilin sa na gina wata gada a Kano
Rotimi Amaechi ya bayyana cewa kwangilar za ta ci Naira Biliyan 13 wajen yasa da kuma sayen sababbin kayan aiki na ceto-rai a ruwan. Dama tun kafin jiya Shugabar NPA Hadiza Bala Usman ta jaddada amfanin wannan yasa.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba ya kasar a halin yanzu don haka Mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo ne ya ja ragamar wannan taron na jiya. Idan aka yashe ruwan zai taimakawa musamman Kudancin Najeriya inji Ministan.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng