Dalilin da ya sanya za a gina Gadar Kasa ta N4bn a jihar Kano - Ganduje
Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Mallam Muhammad Garba, ya bayyana cewa gwamnatin gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta na gina wata katafariyar gadar kasa ta Dangi dake tantagwaryar birnin Kano domin rage cunkoso da jerin gwanon motoci.
Legit.ng ta fahimci cewa, kwamishinan ya bayyana hakan ne yayin ganawar ranar Larabar da ta gabata da manema labarai a babban birnin kasar nan na tarayya.
Mallam Muhammadu yake cewa, babbar manufa ta wannan gadar kasa ita ce kawo karshen cinkoso gami da rage jerin gwanon motoci a hanyar ta Dangi.
KARANTA KUMA: Dalilin da ya sanya rashin tsaro ke ci gaba a Najeriya - Wike
Kwamishinan ya kuma yi watsi da sukar wasu daidaikun mutane dake ganin ya kamata a watsar da aikin gadar domin cimma wata manufa ta su ta daban.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, wannan katafaren aiki ya fara kafuwa ne da sanya hannun gwamna Ganduje bayan da ya samu amincewar majalisar zantarwa ta jihar a zaman ta na 111 da ta gudanar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng