Wutar lantarki: Najeriya za ta hada-karfi da sauran kasashen Afrika
- ‘Yan Najeriya za su samu damar sayen wuta daga kasashen ketare
- A shekara mai zuwa ne za a fara saidawa kasashen Afrika lantarki
- Shugaban Hukumar TCN dai yace za ayi adalci wajen cinikin wutan
Mun samu labari daga Jaridar This Day cewa Najeriya ta fara shirin hada-kai da sauran kasasshen Yammacin Afrika domin karfafa wutan lantarki zuwa shekara mai zuwa. Dama dai samun gas ne yake ba Najeriya ciwon kai.
Shugaban Hukumar TCN masu raba wuta a Najeruya wanda kuma shi ne Shugaban WAPP wanda ke kula da wutan Afrika ta Yamma watau Usman Muhammad yace a watan Yunin 2018 za a hada layin wutan da zai rabawa Kasashen Afrika.
KU KARANTA: Tattalin arzikin Najeriya na habaka a mulkin Buhari
Hukumar ta WAPP za ta hada kai ne da sauran Hukumomin wuta domin ganin an fara samun wutan da za a rabawa Kasashen da ke cikin Yankin Afrika ta Yamma. Yanzu haka dai Najeriya na saidawa Nijar da Kasar Benin wutan lantarki.
Idan aka kammala wannan yarjejeniya, Najeriya za ta iya saida wuta ko ta saya daga Kasashen ECOWAS irin su Ghana da Ivory Coast da kewaye. Muhammad ya tabbatar da cewa Najeriya na fama da matsalar samun gas ne a halin yanzu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng