Zanga-zangar dalibai: Yan sanda sun ce ba suyi harbi yayin ga taron dalibai masu zanga-zanga ba
- Tabbas mun tarwatsa dalibban da suka yi zanga-zanga, amma babu wanda muka harba
- wata mata mai ciki ce tazo wucewa ga kuma jini ya fara zuba, don haka dole mu nema mata hanya don kar rayuwarta ta salwanta
Rundunar yansada ta jihar Ondo, ta bijirewa rahotan da yace jami’an hukumar sun yi harbi ga dalibai yayin da suke gudanar da zanga-zanga a ranar Litinin a garin Akure, yayin da daliban jami’ar ke nuna rashin amincewarsu da sabon tsarin makarantar.
kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa, daliban na jami’ar Adekunle Ajasin dake garin Akungba-Akoko, sun hau tituna domin gudanar da zanga-zangar karin kudin makaranta da jamia’ar tayi shirin yi daga N33,000 zuwa N180 ko N220,000.
Kwamishinan yan sanda na jihar ta Ondo, Olugbenga Adeyanju ya bayyanawa manema labarai a jiya Talata cewa, sunyi amfani ne da matsakaicin karfi yayin da daliban suke gudanar da zanga-zangar. Haka zalika rahotannin dake cewa sunyi harbi yayin zanga-zangar ba gaskiya bane, domin har yanzu ba wani dalibi ko wani wanda yace yaji ciwo.
KU KARANTA: Abubuwa 8 da ka iya baiwa shugaba Buhari nasara a 2019
“Cikin ikon Allah da jajircewar jami’anmu da kuma hadin kan mutanen Ondo, mun shawo kan lamarin yadda ya kamata. Kuma inda ace an harbi wani kamar yadda daliban suka ce, da tuni ku yan jarida kun samu labara.” Inji Adeyanju.
Kwamishinan yan sandan ya kara da cewa, “Ni da kaina naje wurin, kuma abinda ya faru shi ne, na bayar da umarnin a harba wa daliban hayaki mai sanya hawaye domin a tarwatsa su su bar wurin, sakamakon wata wata mai ciki da tazo wucewa zuwa asibiti, kuma tana zubar jini, shi ne na bayar da umarnin a kau da su daga hanya domin kada zanga-zangar tayi sanadiyyar salwantar rayuwarta da dan cikinta. Amma babu wanda yaji ciwo kuma babu wanda aka harba.”
Ina kira ga mutanen da yankin da abin ya shafa da su fito su cigaba da gudanar da harkokinsu kamar yadda suka saba, domin komai ya koma yadda yake , babu sauran hayaniya. A cewar Kwamishinan yan sandan.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng