Dan girman Allah ku tayani addu’an Allah ya bani Fati Washa - Matashi
Kamar yadda kuka sani jaruman fina-finan Hausa kan samun dunbin masoya musamman ma jarumai mata.
Hakan ce ta kasance lokacin da wani matashi ya nuna kudirinsa na son mallakar jaruma Fati Washa.
Fati dai ta kasance daya daga cikin manyan jarumai mata na Kannywood wadanda tauraronsu ke haskawa.
Matashin wanda baa bayyana sunasansa ba ya bukaci a taya shi da addu’a domin Allah ya bashi Fati.
KU KARANTA KUMA: Tafiyan Landan: Dalilin da yasa Buhari bai rubuta wasika ga majalisar dokoki ba
Ya rubuta “Allah ka Bani Fatee Washa” a jikin kwali ya nunawa Duniya ta gani.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng