Masana Ilimin Kimiyya sun gano kasar Sifaniya na girgiza a duk lokacin da Messi ya ci Kwallo
Wani sabon bincike wanda masana da kwararru a fagen ilimin Kimiyya da fasaha sukagudanar ya gano cewa a duk lokacin da fitaccen dan kwallon kafa, Lionel Messi ya ci kwallo, sai kasa ta girgiza.
BBC Hausa ta ruwaito a duk lokacin dan wasan dake taka leda a kungiyar Barcelona dake kasar Sifen da kuma kasarsa Argentina ya ci kwallo, kasar birnin Basalona na girgiza, kamar yadda masanan suka tabbatar.
KU KARANTA: Barayin shanu dauke da muggan makamai sun kai hari a jihar Kaduna, sun jikkata mutane 3
Shugaban masu binciken, Dakta Jordi Diaz ya bayyana cewar sun yi amfani da na’ura ne wajen gano wannan lamari, inda yace sun ajiye na’urar a cibiyarsa, kimanin mita 500 daga filin wasa na Barcelona, Camp Nou, amma duka hak kasar na girgiza sa’dda yan kallo ke murnar cin kwallon Messi.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito masanan na cewa karfin makin na’urar na tashi sosai, a lokacin da yan kallo suka mike suna murnar cin kwallon Lionel Messi.
Daga karshen gungun masu binciken sun tabbatar da cewar girgizar kasar da ake a lokacin da Messi ya ci kwallo, yayi daidai da irin wanda ake yi a duk lokacin da motoci suke bin hanya, da kuma tafiyar jirgin kasa.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng