FIRS tare da hadin gwiwar hukumar EFCC sun gano N29bn
- Hukumar kula da haraji tareda hukumar kula da tattalin arzikin Najeriya sunce zasu kara dangantakar dake tsakani don zakulo mutane ko kamfaninnika da basa biyan haraji
- Dangantakar zata mayar da hankali akan kungiyoyi masu hakkin biyan haraji ga gwamnatin tarayya
- FIRS tare da hadin gwiwar EFCC sunyi nasarar gano kudade N29bn na haraji da aka ki biya daga bankuna da kuma kamfaninnika dake fadin kasar nan
Hukumar kula da haraji tareda hukumar kula da tattalin arzikin Najeriya sunce zasu kara dangantakar dake tsakani don zakulo mutane ko kamfaninnika da basa biyan haraji.
Dangantakar zata mayar da hankali akan kungiyoyi masu hakkin biyan haraji ga gwamnatin tarayya, hukumar ta hada kungiyar kididdigar dukiya don sanin harajin da ya kamata a karba a kanta.
Hukumar FIRS tare da hadin gwiwar EFCC sunyi nasarar gano kudade N29bn na haraji da aka ki biya daga bankuna da kuma kamfaninnika dake fadin kasar nan, daga watan Nuwamba na shekarar 2017 zuwa ga watan Maris 2018, inji Wahab Gbadamosi, mai magana da yawun hukumar harajin.
A ranar Talata, wurin taron da akayi a helikwatar EFCC a birnin tarayya, Wahab Gbadamosi, yace ciyaman na hukumar kula da haraji, Tunde Fowler, yace Najeriya kamar sauran kasashen duniya, tana kokarin habbaka tattalin arzikinta kuma bazata lamunci wadanda basa biyan harajin ba.
KU KARANTA KUMA: Tafiyan Landan: Dalilin da yasa Buhari bai rubuta wasika ga majalisar dokoki ba
Ciyaman na hukumar EFCC, mai rukon kwarya, Ibrahim Magu, yace hukumar zatayi bakin kokarinta don ta kamo masu laifi kuma ta hukuntasu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng