Nigerian news All categories All tags
Babban Malamin Shi’a da yake tsare a Najeriya ya kamu da cutar glaucoma

Babban Malamin Shi’a da yake tsare a Najeriya ya kamu da cutar glaucoma

- Shehin Malamin Shi’a Zakzaky ya kamu da cutar glaucoma a idanu

- ‘Diyar Shehin mai suna Suhaila ta bayyanawa Jaridar Alahed haka

- Cutar ido na Glaucoma na iya jawo mutum ya daina gani har abada

Labari na zuwa mana daga Alahed News na kasar waje cewa Shugaban Kungiyar IMN ta Mabiya Shi’a a Najeriya watau Sheikh Ibrahim Yakub Zakzaky na fama da wata muguwar cuta yanzu.

Babban Malamin Shi’a da yake tsare a Najeriya ya kamu da cutar glaucoma

Zakzaky na fama da wata muguwar cuta yayin da yake daure

Jaridar ta kasar waje ta rahoto cewa ‘Diyar Zakzaky mai suna Suhaila Ibrahim Zakzaky ta bayyana cewa Mahaifin na ta ya samu matsalar nan ta glaucoma ta idanu wanda ka iya jawo masa cutar makanta ta har-abada idan aka yi sake.

KU KARANTA: Kasar Saudi tayi wa masu fama da makanta magani a Kano

Yarinyar Malamin ta bayyana cewa duk da Shehin Malamin yana samun ganin Likita a inda yake tsare, sai dai bai samu isasshen kulawar da ta dace ba a kasar. Cutar ta glaucoma dai idan ta rika ba ta da wani magani a Duniya.

Kwanaki dai Zakzaky ya fito Duniya ta gan shi har yayi wa jama’a bayanin halin da yake ciki amma ya tabbatar da yana samun lafiya. Fiye da shekaru 2 kenan Gwamnatin Najeriya na cigaba da tsare Zakzaky da Iyalin sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel