Dandalin Kannywood: Ni da duk wanda na isa da su ba zamu sake zabar Buhari ba – Abubakar Sani

Dandalin Kannywood: Ni da duk wanda na isa da su ba zamu sake zabar Buhari ba – Abubakar Sani

- Abubakar Sani, fittacen mawakin Hausa ya nuna adawarsa da shugaba Buhari

- Ya ce shi ba zai sake zabar Buhari ba

- Haka zalika duk wadanda ya isa dasu bazasuyi Buhari ba

Rahotanni sun kawo cewa fittacen mawakin nan na Hausa, Abubakar Sani yayi raddi ga sake takarar shugaban kasa Muhammadu Buhari karo na biyu.

A cewarsa, nuna cewar zai sake takara ba shi ke nufin cewa dole ne shugaba Buhari ya yi nasarar lashe zabe a 2019 ba. Sannan kuma cewa kamar yadda shugaban kasar keda yancin sake takara haka kowa keda yancin zabarsa ko kuma kin zabarsa.

Rariya ta rahoto cewa Abubakar Sani ya sha alwashin cewa a wannan karoin daga shi har wadanda ya isa dasu bazasu zabi Buhari ba.

Dandalin Kannywood: Ni ba zan sake zabar Buhari ba – Abubakar Sani
Dandalin Kannywood: Ni ba zan sake zabar Buhari ba – Abubakar Sani

Ya ce hidimar da suka yi a zaben 2015 ya isa haka, sun kuma gode da irin kokarinsa saboda haka a baima wani suga irin nasa kamun ludayin.

KU KARANTA KUMA: Wani mutumi ya haura kasashen Duniya 17 domin ya je aikin Umrah

Yace “'YAN BUHARI A DUHU A KASUWAR BUKATA AKE A IYA BAKI DAN ZAI IYA YIN WARI.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng