Hukumar EFCC ta maka yaron wani tsohon gwamna Kotu bisa karkatar da kudi naira biliyan 1.5
Hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta shigar da yaron tsohon gwamnan jihar Filato, Joshua Dariye, Nanle Dariye, gaban Kotu kan bahallatsar naira biliyan 1.5.
Daily Trust ta ruwaito EFCC na tuhumr Dariye kan aikata laifuka guda shida da suka kunshi cin hanci, rashawa, satar kudi, da kuma karkatar da kudin al’umma. Sai dai Dariye ya musanta tuhume tuhumen a gaban Alkalin babbar Kotun tarayya, mai shari’a Ijeoma Ojukwu.
KU KARANTA: 2019: Makarfi, Balarabe Musa sun yi raddi ga burin Buhari na sake tsayawa takarar shugaban kasa
Jin hakan ta sanya Alkalin dage sauraron karar zuwa 27 ga watan Afrilu, da kuma 10 ga watan Mayu, don fara shari’ar ganga ganga, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.
Ida za’a tuna, a ranar 27 ga watan Feburairu ne hukumar EFCC ta fara gurfanar da Dariye a gana Kuliya manta sabo, tare da Otal dinsa mai suna ‘Apartment le Paradise’, sakamakon wata cinikayya da aka yi ta asusun bankin Otal din, da suka kai na naira biliyan 1.5.
A cewar EFCC, Otal din ba ta da hurumin da za’a sanya mata makudan kudade a asusunta, inda ta kara da cewa naira miliyan 10 ne kacal iya abin da aka yarje ma Otal da yi harka da su, don haka laifin ya saba ma sashi na 5 (1) (a) na kudin laifukan da suka shafi kudi.
Daga karshe Alkalin ya bada belin Dariye akan kudi naira miliyan 5, tare da mutane biyu da zasu tsaya masa, suma zasu ajiye naira miliyan 5.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng