Sinadaran abincin 4 dake bunkasa garkuwar jikin masu cutar kanjamau

Sinadaran abincin 4 dake bunkasa garkuwar jikin masu cutar kanjamau

Kamar yadda hausawa ke mata lakabi da cuta mai karya garkuwan jikin dan adam watau Kanjamau, ta zamo cuta da mutane suka fi jin tsoron kamuwa da ita.

Harma wasu kan kirata da kabari salamu alaikum, hakan ya sa mutane ke cike da kyamar duk wanda aka tabbatar yana dauke da wannan cuta.

Wani likita mai suna Dapo Morawo da ke aiki a asibitin De-Vine a babban birnin Abuja, ya bayyana irin abincin da ya kamata masu cutar kanjamau su dinga ci.

Sinadaran abincin 4 dake bunkasa garkuwar jikin masu cutar kanjamau
Sinadaran abincin 4 dake bunkasa garkuwar jikin masu cutar kanjamau

Ga wasu daga cikinsu a kasa:

1. Abincin dake tattare da sinadarin ‘Proteins’ irin su wake, kwai, madara da sauran su domin suna tamakawa wajen gina jikin mutum.

2. Abincin dake kunshe da sinadarin ‘Carbonhydrates’ na taimaka wa jikin mutum da karfi.

KU KARANTA KUMA: Labari mai dadi: Mata a jihar Bauchi sun samar da hanyar gargajiya ta sarrafawa da adana Tumatir

3. Cin kayan lambu saboda suna kara wa mutum jini a jiki.

4. Ta'ammali da abincin dake kunshe da sinadarin ‘Fats and Oils’ saboda cuko inda rama yake.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng