Mun zama abin dariya a idon duniya: Tsohon shugaban kasar Qatar yayi Allah wadai da nuna goyon bayan Isra'ila da Yariman Saudiyya yayi
- A ranar Larabar nan data gabata ne Hamad bin Jassim Al Thani yayi wata magana a shafin sa na Twitter yace; "kasashen yankin larabawa sun zama 'abin dariya a duniya' tunda sun zama masu furuci don su gamsar da kasashen yamma
A ranar Larabar nan data gabata ne Hamad bin Jassim Al Thani yayi wata magana a shafin sa na Twitter yace; "kasashen yankin larabawa sun zama 'abin dariya a duniya' tunda sun zama masu furuci don su gamsar da kasashen yamma.
DUBA WANNAN: Aikin gadar sama ta jihar Kano shine abinda jama'ar jihar suka fi bukata - Gwamnatin jihar Kano
Mun zamo abin dariya da muke wulakanta dukiyar mu akan abubuwa marasa amfani. Cewar Sheikh Hamad.
"Mun fada cewa isra'ilawa suna da hakkin zama a kasashen su hankali kwance, wanda hakan shine matsaya ta a shekaru da dama kuma har yau ina kan wannan maganar, kuma suna kunyar su fadi hakan. Palestinawa ma suna da damar fada amma tsoro ya mamaye musu zuciya.
"Ya kamata mu fadi hakan kuma muyi abinda mutanenmu suke tsammani. Muna bukatar wanda zai kare mu daga ci baya da kuma wulakancin da kasar nan take fuskanta ba wai abinda zai gamsar da wasu ba."
Sheikh Hamad ya kara da cewa kasashen yankin larabawa dole ne su gyara dangantakarsu saboda amfanin mutanen yankin.
A wata tataunawa da yayi da wata jarida ta kasa Amurka wacce ta fito ranar Litinin. Magajin Saudi Mohammed bin Salman ya fito ya nuna cewar suna goyon bayan kasar Isra'ila. "Na tabbata cewa kowace al'umma a duk inda suke suna da damar zama lafiya a kasar su," inji Yariman.
Sarkin Saudiyyan Salman ya hanzarta kin amincewa da furucin Dan nashi.
A ranar talata ne sarkin ya kara jaddadawa " har yanzu masarautarshi na nan akan bakanta game da Palestinawa da kuma halattattun hakkokinsu na dogaro da kansu.
Furucin Yariman ya kawo tashin hankali a Palestine, inda sojojin Isra'ila suka kashe Palestinawa 16 a satin da ya gabata a zanga zangar lumana da sukayi a tsakanin Israel da Gaza.
A watan yuni na shekarar da ya gabata, Saudi Arabia, Bahrain, Egypt da kuma daular larabawa wato UAE suka tsinke dangantakarsu da Qatar, wadanda ake zargin ta da goyon bayan bata garin musulmai. Sai dai kasar ta musanta zargin.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng