Aikin gadar sama ta jihar Kano shine abinda jama'ar jihar suka fi bukata - Gwamnatin jihar Kano

Aikin gadar sama ta jihar Kano shine abinda jama'ar jihar suka fi bukata - Gwamnatin jihar Kano

- Sabanin maganganun da jama'a suke yi a jihar Kano, gwamnatin jihar Kano ta ce aikin N4.5b na gadar sama da zata yi, shine yayi dai dai da abinda mutanen jihar suke bukata

- Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba, shine ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, ya ce wadanda ke sukar aikin suna yin hakane bisa rashin sani

Aikin gadar sama ta jihar Kano shine abinda jama'ar jihar suka fi bukata - Gwamnatin jihar Kano
Aikin gadar sama ta jihar Kano shine abinda jama'ar jihar suka fi bukata - Gwamnatin jihar Kano

Sabanin maganganun da jama'a suke yi a jihar Kano, gwamnatin jihar Kano ta ce aikin N4.5b na gadar sama da zata yi, shine yayi dai dai da abinda mutanen jihar suke bukata.

Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba, shine ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, ya ce wadanda ke sukar aikin suna yin hakane bisa rashin sani.

DUBA WANNAN: Babban bankin Najeriya yace ya kashe N5b akan harkar bunkasa noman shinkafa

Ya ce, "Bincike ya nuna rashin fahimtar inda aikin gwamnatin yasa gaba ta hanyar wasu mutane masu nuna son zuciya, wadanda suke nuna rashin amincewar su akan aikin gadar sama ta shatale-talen Dangi," inji shi.

Garba ya kara da cewar aikin wanda aka amince dashi a taron majalisar zartarwa na 111 da aka gabatar, gwamnatin ta kuduri yin aikin ne bisa la'akari da irin cinkoson ababen hawa da ake samu a wurin.

"Abin bakin ciki shine, wasu mutanen da basu da kishi a jihar nan suna ta kushe aikin, saboda son rai da kuma sabanin ra'ayi na siyasa, inda suke zargin cewar gwamnati tana aiwatar da wannan gagarumin aikin ne ba tare da ta saka shi a cikin kasafin kudi ba," inji shi.

Kwamishinan ya bukaci jama'ar jihar Kano dasu yi watsi da duk wani dan siyasa da yake son ganin ya raba kan al'umma saboda wata biyan bukata tashi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel