Alamu guda 8 a jikin dan Adam dake nuna kamuwa da cutar shanyewar rabin fuska
Wani daga cikin matsalar da marasa lafiya ke fama da shi, shi ne na mutuwar wani sashi daga cikin sassan jikin dan Adam, misali, kamar shanyewar wani barayi na fuskar mutum, kamar yadda wani likitan kasha Dakta Hamdan Usman ya bayyana.
Likitan yayi bayanin shanyewar barin fuska kamar haka: “Shanyewar ɓarin fuska larura ce da ke faruwa sakamakon matsala a jijiya ta bakwai(7) da ta fito daga ƙwaƙwalwa zuwa fuska. Wannan jijiya ka iya samun matsala kamar shaƙewa, dannewa, rauni daga ƙwayayyakin cuta ko bugu daga waje akan hanyarta da ta fito daga ƙwaƙwalwa zuwa fuska domin kaiwa da komowar saƙonni a fuska, jakar yawu (miyau), jakar hawaye, tsinin harshe, da wata tsoka mai daidaita sauti da ke can cikin kunne”
KU KARANTA: BWani Bom ya tashi a jihar Osun, yayi raga raga da wani gidan sama
Don haka matukar daya daga cikin wadannan matsaloli ya faru, jijiyar za ta yi sanyi, a sanadin haka fuskar zata shanye, ga wasu alamomin dake nuni da kamuwa da cutar shanyewar rabin fuska:
1) Samun matsalar bayyana labarin zuciya a fuska kamar murmushi da sauransu
2) Sakkowar gira da kuma yawan hawaye
3) Zubowar yawu ta ɓarin da bakin ya shanye
4) Kasawa ko wahalar rufe ido sosai
5) Karkacewar baki: wanda zai sa wahalar rikewa ko zirarewar abinci ko abin-sha daga baki
6) Matsalar kasa ɗaga gira ko tattare fatar goshi
7) Rashin jin ɗanɗano a tsinin harshe
8) Ƙaruwar ƙara ko sauti a kunne daya
Haka zalika akwai wasu cututtuka da ka iya kawo sanadin shanyewar barin fuska, da suka hada da:
1) Bugu/rauni a kai/fuska
2) Ciwon kunne
3) Ɓarkewar jijiyar jini a cikin kai
4) Ciwon Siga
5) Matsananciyar mura
6) Shanyewar barin jiki
7) Doguwar tafiya a kan abin hawa tare da iska mai karfi tana bugun ɓarin fuska
Wannan cuta na sanya yawancin mutanen da suka kamu da shi kauracewa ma jama’a don jin kunya ko kuma gudun tsangwama, don haka ake kira ga duk wanda ya kamu ya garzaya Asibiti domin samun ingantaccen kulawa daga kwararren likitan kashi, wato ‘Physiotherapist’ a turance.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng