Duba kaga yawan littattafan da Shehu Dan Fodiyo ya rubuta
- Wani mawallafin littafin "Intellectual Foundation of Sokoto Caliphate", ma'ana Kafa Daular Usmaniyya bisa ilimi da basira, Malam Abdullahi Bukhari Sakkwato, ya bayyana cewar ya tattara bayanai da yawa game da tarihin daular Usmaniyya saboda tsananin kishi da yake dashi akan ya sanar da duniya tarihin daular
Wani mawallafin littafin "Intellectual Foundation of Sokoto Caliphate", ma'ana Kafa Daular Usmaniyya bisa ilimi da basira, Malam Abdullahi Bukhari Sakkwato, ya bayyana cewar ya tattara bayanai da yawa game da tarihin daular Usmaniyya saboda tsananin kishi da yake dashi akan ya sanar da duniya tarihin daular.
"Littattafan da Shehu Dan Fodiyo ya wallafa sunfi 250, kawai dai an samu matsalar rashin adani mai kyau ne, shine dalilin da yasa wasu da yawa daga cikin su suka salwanta.
"Na tattara bayanai masu dinbin yawa wadanda na samo daga gidajen tarihi da kuma gidan wazirin Sakkwato, da kuma sauran manyan masana dake Sakkwato."
DUBA WANNAN: Sojoji sun kama wani dan leken asirin 'yan ta'adda akan hanyar Takum zuwa Chanchangi
Ya bayyana cewar, "A takaice dai na samu littattafan Marigayi Shehu Usman Dan Fodiyo fiye da 147."
Sannan kuma ya ce ya tattaro bayanai da yawa game da tarihin rayuwar Sarkin Musulmi Muhammadu Bello da Abdullahin Gwandu: "Na tattara wasu bayanai da suke nuni da littattafan da sarkin Musulmi Muhammadu Bello ya rubuta wanda sun kai 180, sannan na Abdullahin Gwandu kuma sun kai 187."
Mawallafin yayi bayanin cewar litaffin ya tabo dukkanin sassa na tarihin Daular Usmaniyya: "Wannan littafi ya tabo lokacin jihadi har zuwa tarihin shugabanni da kuma wadanda suka kafa daular nan."
"Akwai tarihin sarakunan arewa su kimanin 17, da kuma tarihin shahararrun malamai da suka yi manyan rubuce-rubuce a fannin bunkasa addinin da kuma harkar siyasa a cikin daular."
Littafin ya kunshi tarihin dukkan sarakunan musulmi tun daga Shehu Usman Dan Fodiyo zuwa kan wanda ya ke kai yanzu.
"Akwai tarihin masarautar Gwandu, har ma da tsarin sarakunan da ke nada sarkin musulmi," inji shi.
Ya bayyana cewa ya wallafa littafin ne saboda kishin da yake da shi na Daular Usmaniyya da Shehu Usman Dan Fodiyo ya kafa cikin ilimi da hikima a wannan yanki na Afirka.
Ya kuma ce ya wallafa wannan littafi ne a shekarar 2015, kafin aka wallafa shi daga baya.
Malam Abdullahi Bukhari Sakkwato, na tare da Kwalejin Shehu Shagari da take Sakkwato a Najeriya.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng