Nigerian news All categories All tags
Sojoji sun kama wani dan leken asirin 'yan ta'adda akan hanyar Takum zuwa Chanchangi

Sojoji sun kama wani dan leken asirin 'yan ta'adda akan hanyar Takum zuwa Chanchangi

- A wani yawon atisaye da rundunar sojin Najeriya ta bataliya 93 ta yi ranar Lahadi dinnan 8 ga watan Afilu, rundunar tayi nasarar kama wani dan leken asirin 'yan fashi, a lokacin da yake kokarin nuna wani wanda suke so su kashe a mota

Sojoji sun kama wani dan leken asirin 'yan ta'adda akan hanyar Takum zuwa Chanchangi

Sojoji sun kama wani dan leken asirin 'yan ta'adda akan hanyar Takum zuwa Chanchangi

A wani yawon atisaye da rundunar sojin Najeriya ta bataliya 93 ta yi ranar Lahadi dinnan 8 ga watan Afilu, rundunar tayi nasarar kama wani dan leken asirin 'yan fashi, a lokacin da yake kokarin nuna wani wanda suke so su kashe a mota.

DUBA WANNAN: Sarkin Musulmi ya gargadi matasa akan bangar siyasa a zaben 2019

Anji mutumin da ake tuhuma din suna zancen wani mai suna Malam Musa Ibrahim da niyyar zasu kashe shi, akan wani dalili da shi kadai ne ya sani. Sai dai basu samu damar yin hakan ba, domin kuwa an bayyana wa rundunar sojojin a asirce, inda su kuma suka kamo wanda yake kokarin kai labarin.

Yayinda ake tuhumar sa, ya bayyana cewar yana daya daga cikin masu kai bayani ga 'yan ta'addan dake yankin. A yanzu haka dai wanda ake zargin yana hannun rundunar sojin ana cigaba da gabatar da bincike akan shi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel