Nigerian news All categories All tags
Aikin bir inji tusa - Don Pastocin Arewa son ce a zabi Buhari babu abinda hakan zai kara masa - PDP

Aikin bir inji tusa - Don Pastocin Arewa son ce a zabi Buhari babu abinda hakan zai kara masa - PDP

- PDP bata ji dadin goyan bayan da Buhari ya samu daga Kungiyar Pastocin Arewa ba

- Jam'iyar PDP tace, duk karya ne ba abinda kungiyar Pastocin Arewa zasu iya maka

A cikin satin da muke bankwana da shi ne, wata kungiyar Pastocin Arewa na Jihohi 19 suka kaiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari ziyara a fadarsa dake Abuja, inda a yayin waccan ziyar suka nuna yabo ga irin tsare-tsaren da gwamnatinsa keyi wajen farfado da tsaro da kuma tattalin arzikin kasar nan, kana suka bayyana aniyarsu ta goyon bayansa a idan har yace zai tsaya takara a 2019.

Kungiyar Pastocin Arewa ba su da ikon cewa a zabi Buhari PDP

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ke gaisawa da Pastocin Arewa

Sai dai kuma za’a iya cewa waccan ziyar ba ta yiwa babbar jam’iyyar adawa ta PDP dadi ba, idan akai la'akari da kakkausan martanin da jam'iayar ta mayar ga fadar shugaban kasar a yau Lahadi, ta bakin sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa Mr. Kola Ologbondiyan a garin Abuja.

KU KARANTA: Duk karya ce: Sanata Goje ya yi fata-fata da shirin gwamnatin Buhari

Kungiyar Pastocin Arewa ba su da ikon cewa a zabi Buhari PDP

Babban sakataren yada labarai na PDP Kola Ologbondiyan

A cewar PDP "Ba yau gwamnatin APC ta saba shirya irinwasan kwaikwayo ba, domin a baya ma sun yi haka da sunan neman goyon baya, inda aka baiwa shugaban kasa lambar girmamawar da ta jawo cece-kuce da sunan Martin Luther King Jr."

"Sakamakon kushe yanayin salon mulkinsa da manyan mutane daga kasashen duniya su keyi irinsu Bill Gate da Martin Luther Kings Jr group su keyi, shi ne yanzu gwamnatin APC ta dawo cikin gida waje kananan kungiyoyin da ba wanda ya sansu." Kola bayyana.

Abin takaici ne irin abinda wadancan masu amfani da sunan addinin su kayi, domin hatatta uwar kungiyarsu ta kasa CAN, ta ce ba da yawunta su kayi wancan batu ba. a cewar sakataren na jam'iyyar ta PDP.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel