Ashe Ruwan shan mu na Rijiyoyin Burtsatsai na iya gurɓata da kwayoyin cuta sama da 10m na Bahaya

Ashe Ruwan shan mu na Rijiyoyin Burtsatsai na iya gurɓata da kwayoyin cuta sama da 10m na Bahaya

A wata sabuwar kididdiga da majalisar dinkin duniya ta fitar ta bayyana cewa, a halin yanzu kimanin kaso 64.1 cikin 100 a Najeriya ke samun tsarkakakken ruwan sha a gidajen su.

Wannan binciken da masana kiwon lafiya suka gudanar ya bayyana cewa, akwai yiwuwar kasar Najeriya za ta afka cikin matsanancin kangi na gurbacewar ruwan shan da a wasu lokuta na nan gaba ma su gabatowa muddin ba a dauki wani mataki ba.

Kwararrun masana kiwon lafiya na majalisar dinkin duniya sun bayyana cewa, a halin yanzu kaso 96.3 cikin 100 na fuskantar barazana ta rashin tsaftataccen ruwan sha da ya gurɓata da bahaya da kuma wasu sunadaran gurbatanci na kwayoyin cuta da ake kiran su Escherichia coli (E.coli).

Kididdigar ta bayyana cewa, ana samun gida 1 cikin kowane 4 a Najeriya dake ta'ammali da gurbataccen ruwa sha, inda jihar Imo ta ke kan gaba a duk jihohin kasar da kaso 92.2 na al'ummar ta dake samun tsaftataccen ruwan sha.

KARANTA KUMA: Ajimobi, Ganduje da Okorocha sun shirya tsaf domin yakin shugaban jam'iyyar APC

Binciken ya bayyana cewa, sunadaran E.coli su ne mafi akasarin kwayoyin cuta dake cikin gurbataccen ruwan sha da al'ummar Najeriya ke ta'ammali.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, kwayoyin cutar E.coli su ke haddasa cututtukan amai da gudawa wanda a wani sa'ilin ya kan zo da gudan jini da kuma matsalolin koda ko kuma idan aka yi rashin sa'a rai ya yi halin sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel