Ina kaunar mata ta, amma ba zan iya ci gaba da zama da ita ba - Wani magidanci ya shaidawa Kotu

Ina kaunar mata ta, amma ba zan iya ci gaba da zama da ita ba - Wani magidanci ya shaidawa Kotu

Wani dan kasuwa mai shekaru 39 a duniya, Mista Olasunkanmi Yusuf, ya shaidawa wata kotun al'adu ta Igando dake jihar Legas a ranar Juma'ar da ta gabata cewa, a halin yanzu matar sa ba ta da wuri a gida tun da har ta riga da kama gabanta.

Olasunkanmi yayi wannan furuci a yayin mayar da martani ga korafin matar sa, Beatrice, inda yace ta kama gaban ta bayan wata sa'insa da ta shiga tsakanin su.

A yayin gajen hakuri na zaman jiran dawowar mai dakin sa, Olusunkanmi ya auri wata matar kuma ya mika da daya tilo dake tsakanin sa da Beatrice zuwa ga mahaifiyar sa domin ta ci gaba da kulawa da shi.

KARANTA KUMA: Yadda gasar wasanni ta hukumar Sojin Sama ta kaya a jihar Akwa-Ibom

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, Olasunkanmi ya shaidawa kotun cewa ba ya da halin zama da mata biyu duk kasancewar kauna ta hakika da yake yiwa Beatrice

A sakamakon biyan bukatar ta wannan mata da miji, alkalin kotun Mista Akin Akinniyi ya raba auren dake tsakanin su inda ya umarci Olasunkanmi biyar diyya ta N200, 000 ga Beatrice tare da bashi dama ta ci gaba da rike dan da suka haifa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: