Nigerian news All categories All tags
Dalibai a jihar Adamawa sun yi shirin kawo karshen rikicin Arewa maso Gabashin Najeriya

Dalibai a jihar Adamawa sun yi shirin kawo karshen rikicin Arewa maso Gabashin Najeriya

Daliban makarantun gaba da Sakandire na jihar Adamawa, sun fara tafka muhawarori game da gano hanyoyi na warware matsalolin rikici da kuma kalubale na 'yan gudun hijira da ake fama a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan.

Rahotanni sun bayyana cewa, za a tafka wannan muhawara a tsakanin daliban jami'ar kimiya ta Modibbo Adama dake birnin Yola, jami'ar jihar Adamawa da kuma kwalejin ilimi dake garin Mubi.

Shafin jaridar PM News ya ruwaito cewa, cibiyar fasahar watsa labarai da ci gaba ta CITAD, (Centre for Information Technology Development) tare da hadin gwiwar gidauniyar yankin Arewa maso Gabas ta NERI, (North East Regional Initiative) su suka dauki nauyin gudanar da wannan muhawarori a jihar ta Adamawa.

Sansanin 'yan gudun hijira

Sansanin 'yan gudun hijira

Da yake jawabi a ranar Asabar din da ta gabata yayin taron a birnin Yola, Babban darakta na CITAD Mista Yunus Zakari ya bayyana cewa, an shirya wannan muhawara ne domin samar wa matasa dandali na tattaunawa tare da baja kolin dalilai da za su magance matsalolin da yankin Arewa maso Gabashin kasar nan ke fama.

Mista Zakari yake cewa, za a shirya makamanciyar wannan muhawara ga dalibai a jihar Borno da kuma Yobe, inda ya kara da cewa akwai manufa ta mika dandalin ga matasan dalibai a ƙasashen Chadi, Kamaru da kuma Nijar.

KARANTA KUMA: Yadda gasar wasanni ta hukumar Sojin Sama ta kaya a jihar Akwa-Ibom

Shi kuwa shugaban cibiyar NERI Mista Machill Maxwell, ya bayyana cewa cibiyar tana goyon bayan wannan shiri a yankunan da suka fi tagayyara sakamakon rikice-rikice.

Abin da ya kamata matasa suyi don taimakawa wajen kawo karshen tashin hankali a Arewa maso Gabas;

Legit.ng ta fahimci cewa, ababen da aka tattauna a muhawarar sun hadar da;

"Abinda ya kamata matasa su yi domin taimakawa wajen kawo karshen tashe-tashen hankulla a yankin Arewa maso Gabas."

"Yadda za a janye matasa da masu karancin shekaru daga afkawa cikin rikicin da ta'addanci."

"Wace hanya ce mafi tasiri da ya kamata gwamnati ta bi domin magance hare-hare da ta'addanci."

"Sai kuma irin gudunmuwa da ya kamata daliban gaba da sakandire za su bayar wajen magance matsalolin 'yan gudun hijira."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel