Menene makomar Saudiyya daga canje-canje da ake samu daga Yariman kasar?

Menene makomar Saudiyya daga canje-canje da ake samu daga Yariman kasar?

Wannan rubutu ra'ayin Mubarak Bala ne, ba ra'ayin Legit.ng

- Tun da Sarki Salman ya kwace mulki daga hannun dan-danuwansa ya baiwa dansa ake ganin chanji

- Alkawurran MBS shine cewa zai kawo karshen ta'addanci da zafin kishin addini a kasarsa

- Dama Saudiyya ke daukar nauyin masallatai a duniya, wadanda suka zafafa imanin mutane har wasu ke tayar da jihadi

Menene makomar Saudiyya daga canje-canje da ake samu daga Yariman kasar?
Menene makomar Saudiyya daga canje-canje da ake samu daga Yariman kasar?

A kokarinsa na zaqulo kasarsa daga zazzaan ra'ayi, Yarima mai jiran gado, MBS, ya fara kawo sauye sauye a kasar inda har ta kai ya bude wuraren wasan karta da silima da ma barin mata su wataya duk ida suke so su je.

Menene makomar Saudiyya daga canje-canje da ake samu daga Yariman kasar?
Menene makomar Saudiyya daga canje-canje da ake samu daga Yariman kasar?

A baya ma cikin bara, yace kasar zata toshe wasu Hadisai da za'a daina amfani dasu, wadanda 'yan ta'adda kan yi amfani da su lokutan kai hare-hare kan jama'a da sunan Islama, har ma suyi kabbara, lamari da baya wa musulmi dadi.

Menene makomar Saudiyya daga canje-canje da ake samu daga Yariman kasar?
Menene makomar Saudiyya daga canje-canje da ake samu daga Yariman kasar?

Tun da kasar Iran ta faro irin nata juyin juya halin kasar Saudiyyar ke kokarin farkar da matasa. cikin shekarun 1980s har zuwa yanzu, inda take turo kudade kasashen musulmi don yada wahabiyyanci da ahlussunna, da kore shi'anci.

DUBA WANNAN: Wadanda basu yi bokon kirki ba a Bollywood

Sai dai hakan kuma ya zafafa tsama da ake samu tsakanin dariku daku cikin ita kanta sunnar, wadda ake ganin kafirta juna karara da suke yi a matsayin ummul-aba'isin rarrabuwar kai tsakanin dangogin musulmi.

A karshe dai, kasashe masu yawan matasa da talauci, kari da jahilci, sun koma bin siyasar gabas ta tsakiya, inda sukan kashe junansu domin wannan Iran yake bi wancan Saudiyya yake bi, musamman a arewacin Najeriya.

Shin ko yanzu da Saudiyyar ke kokarin zamewa daga akidar tata, hakan zai koya wa samarin Najeriya da ma malaman zafafa ra'ayi wasu darussa?

Boko Haram dai, babu alama zata tuba, koda kuwa duk sauran Ahlussuna sun yasar da wa'azozi da litattafai masu sanya zafin ra'ayi.

Muna biye.

Ra'ayin Mubarak Bala, Kano.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel