Gas din da Najeriya ke konewa a iska a shekara ya kai na $10b, kamar tiriliyan uku da rabi kenan
- Ana sakin gas dinne domin babu takanoloji ta kama shi a sarrafa
- Gas din dai shine kuma NLNG ke sayarwa da tsada
- Shine kuma na girki da muke kona wa a gida
Gas da ke tsada a Najeriya kuma ke kawo saukin aikin girki dai shi ake barnatarwa shekaru 40 a sararin iskar saman Najriya.
Kama shi yana da wuya, kuma sarrafashi ma akwai tsada, sai dai yana da tsarki sosai, domin bai fiye jawo dumamar yanayi ba, in aka kwatanta shi da kwal ko fetur ko kananzir.
Yanda Najeriya zata iya samun $10 biliyan daga gas da ake rasawa a iska duk shekara.
Manajan shirin siyarda gas ta kasa (NGFCP) wanda ke karkashin ma'aikatar man fetur ta tarayya Mai shari'a Darefaka ya bayyana cewa Najeriya na rasa kusan dala biliyan goma daga kudin dake shigowa sanadiyyar gas din da ake rasawa a iska. Ta yanda ba a iya tara shi da siyar dashi a kasar.
Ya kara da cewa Idan gas din da ake rasawa a iska ana tara shi yanda ya dace, zai iya samar da aikin yi 300,000, zai samarda 600,000MT na LPG a shekara kuma zai samarda 2.5GW na wutar lantarki.
A taron da aka a Legas na cibiyar kasuwanci ta Norwegian da ke najeriya (NNCC) mai taken "tatsar kudi daga gas: yanda yake da damar da ake da ita a masana'antar gas ta Najeriya" Darefaka ya bayyana cewa yanzu Najeriya tana amfani da kusan 700mmscf na gas domin samar da wutar lantarki, wanda za a iya rubanya shi ta hanyar tarawa da siyarda gas din da ake rasawa a iska. Yace an kusa tabbatar da dokoki akan gas din da ake rasawa a iska nan ba da dadewa ba. Ya jaddada cewa dokokin ba al'ummar Niger delta kadai zasu amfana ba, har tattalin arzikin Nigeria.
DUBA WANNAN: Yan Indiya da basu yi wata bokon kirki ba
Manajan Midstream, seven energy Ian Brown Peterside ya tabbatar da cewa Amfani da ma'adanai na iskar gas na kasar nan ba karamin cigaba ze kawo ba nan gaba.
Tabbatacciyar iskar gas ba karamar fa'ida zai kawo ba ga habakar tattalin arziki, wutar lantarki dindindin wanda zai kawo cigaba ga bangarori da dama na kasar.
Ya kara da cewa rashin wutar lantarki ya kawo tawaya ta bangaren zuba sababbin hannayen jari da kuma rike wadanda ake dasu a kasar.
John Chibueze, abokin kasuwancin Adepetun Caxton-Martins Arbor and Segun (ACAS Law) ya kara dukan Jan aikin da Gwamnatin ta ke yi domin bunkasa haka, habaka da siyarda gas.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng