Gwamnatin Najeriya ta koma tatsar kudin caca saboda lalitar ta tayi kasa

Gwamnatin Najeriya ta koma tatsar kudin caca saboda lalitar ta tayi kasa

- Najeriya ta dogara ne da arzikin man fetur

- Farashin man fetur ya zube warwas a fadin duniya

- Yanzu kasar ta fara neman kudi ta wasu hanyoyin daban

Gwamnatin Najeriya ta koma tatsar kudin caca saboda lalitar ta tayi kasa
Gwamnatin Najeriya ta koma tatsar kudin caca saboda lalitar ta tayi kasa

Gwamnatin tarayya zata waiwayi caca sakamakon faduwar kudaden shiga na mai. Sakamakon koma bayan da aka samu na kudin shiga na mai a kasar, Gwamnatin tarayya tace zatayi duk abinda dan'adam zai iya domin ta farfado da fannin caca a cikin hanyoyin farfado da samuwar kudin shiga na kasar.

Sakataren gwanatin tarayya mai kula da muhimman aiyuka ya sanar da hakan a ofishin Sakataren Gwamnatin tarayya, Chief Williams Alo, taron kaddamarwa da kuma kuma bada taimakon tallafin akwatinan magunguna na bada tallafin gaggawa ga makarantun sakandare na Gwamnati a Abuja wanda National Lottery Trust Fund (NLTF) ta dauka nauyi

Alo, wanda shine babban bako a gurin taron, yace a lokutan farko na wayewar Dan'adam, kudin da aka samu daga caca sunyi amfani gurin canza al'umma gurin samarda ababen more rayuwa.

DUBA WANNAN: Zamfara ce ta-kashin baya a harkar Boko a duniya

A sakamakon wannan aikin da NLTF tayi a yau, ta tabbatar ma da yan'najeriya cewa caca tana amfani,yan najeriya sai mu tashi tsaye domin kuwa Gwamnatin tarayya ta kara kawo wata hanyar ta chanji

A sakamakon fadin kudin shiga na mai wanda abubuwa da suka kunshi rashin zaman lafiya a duniya, faduwar tattalin arziki na duniya da kuma samun mai a kasashen da suke siyan mai, bukatar nemo wasu hanyoyin kudin shiga dole ne.

Caca kuwa na daya daga cikin hanyoyin da Gwamnati ta samu, tafi kuma zama abin dogaro.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: