Dandalin Bollywood: Aftawan Indiya da basu yi karatun boko ba
Da yawa daga cikin jaruman fina finan India suna da karancin ilimin boko. Abin zai Baku mamaki idan kukaji cewa wasu daga cikin jaruman India suna da karancin ilimin boko duba da yanda jaruman sukayi suna a duniya.
Daga cikin su kuwa akwai
AKSHAY KUMAR
Akshay ya fara halartar wata makaranta me suna Don Bosco daga bisani ya koma wata makaranta a Mumbai ta India.bayan wani lokaci sai yabar makaranta gaba daya.
Daga nan akshay ya koma makarantar koyon fada da kare kai a garin Bangkok.
Jarumin yana da takardar shedar zama dan kasar Cana
KAJOL
Ta kasance daga cikin jaruman da sukayi fice a duniya. Ita dai wannan jaruma diyace ga jarumi Tanuja Samarth. Kajol ta fara karatun ta ne a makarantar kwana ta St.Joseph Convet dake Panchgani. Daganan ta tsunduma harkar film tanada shekaru 16 a duniya.Kajol taso komawa karatu saidai hakan bata samu Ba.
SALMAN KHAN
Salman khan ya fara karatunsa a babbar makarantar nan ta St.Stanislaus dake Bandra a Mumbai yayin da koma kwalejin Elphinstone wanda yabar makarantar a shekarar sa ta biyu.
Salman khan ya fito a fina finai da dama.
KATRINA KAIF
Ta kasance ba mazauniya ce a guri daya ba wannan shiya hanata ci gaba da karatu.sanda take kan kuruciyar ta ta kasance tana tallata kayan kawa wato modelling.
Katrina tana daga cikin matan dake daukar albashi me tsoka a Bollywood.
RANBIR KAPOOR
Ya kasance bashi da sha'awar karatu wannan ya zanyo masa zama koma baya a makarantar Bombay Scottish school dake mahim.
Ranbir yana daga cikin fitattun jaruman India
ASHWARYA RAI
Ashwarya ta halarci makarantu biyu kafin daga bisani ta koma kwalejin DG Ruparel dake Matubata
Da farko taso karantar aikin likita amma hakan bata samu ba saita canja da koyon zane zane.
Ashwarya rai ta kware a harkar rawa tun tana da shekara 10. An taba zabar ta sarauniyar kyau a shekara ta 1994.
AMIR KHAN
Amir khan ya fara karatun sane a makarantar J.B petit school,daganan ya wuce St.Anne's high school dake bandra.jarumin ya halarci makarantar Bombay Scottish dake mahim.
Ya kammala karatunsa na kwaleji.a yayin da yake babbar makarantar ya kware wajen buga kwallon kafa da tennis domin kuwa har fice yayi a lokacin.
Amir khan yanada magowa ba ya India.
PRATEIK BABBAR
Yayi makarantu biyu kafin ya koma St.Andrew kafin daga bisani ya dena zuwa gaba daya.
Prateik yana daga cikin matasan Bollywood.
DUBA WANNAN: Zamfara ce ta-kashin baya a harkar Boko a duniya
SRIDEVI
Ta fara film ne tun tana yarinya hakan shiya zanyo bata samu damar yin karatu ba.
Sridevi ta rasu a 24 ga watan fabrairun shekarar na.
DEEPIKA PADUKONE
Ta samu nasarar kammala kwalejin share fagen shiga jami'a ta Mount Carmel.daga nan ta shiga jami'ar Indira Gandhi inda take karanta ilimin zamantakewar Dan Adam.
Daga bisani itama tabar karatun ta maida hankali akan sana'ar ta.
Deepika ta karbi kyaututtuka da dama a harkar film
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng